(ABNA24.com) Kawancen kungiyoyin musulmi a Malawi MAM ya nuna rashin amincewa da matakin hana saka lullubi a wata makaranta a kasar.
Makarantar Agalican ta sanar da cewa dalibai masu saka hijabi a makaranta su daina.
Wannan mataki bai tsaya nan ba, domin kuwa makaranta ta kafa dokar hana daukar duk wata daiba da ta saka lullubi a kanta a wannan makaranta.
Sheikh Dinala Chubulika kakakin MAM ya bayyana cewa, ba za su amince da aka ba, kuma suna kira ga gwamnatin kasar da ta gaggauta daukar matakin taka wa wanann makaranta burki kan hakan.
Duk da umarnin da gwamnati ta bayar na hana korarar dalibai mata masu sanye da lullubi, wannan makaranta tana ci gaba da yin biris da umarnin gwamnatin kasar ta Malawi.
/129
26 Nuwamba 2019 - 07:33
Lambar labari: 989389
Musulmi a kasar Malawi sun nuna rashin amincewa da matakin hana saka lullubi a wata makaranta a kasar Malawi.